ABNA24 : Jaridar Time Line ta kasar Ruwanda ta bayyana cewa ministan harkokin wajen na kasar Faransa Jean –Yves Le Drian da tokoransa na kasar Ruwanda Vincent Biruta ne suka sanya hannu a kan yarjejeniyar a gaban shuwagabannin kasashen biyu.
Banda haka gwamnatin kasar Faransa ta nuna alluran riga kafin cutar korona 100,000 wanda shugaban kasar ta Faransa ya zo da su a cikin jirginsa a matsayin tallafi ga kasar Ruwanda don yaki da cutar.
Har’ila yau kasashen biyu san sanya hannu a kan yarjejeniyar aiki tare a fagen wasannin da watsa kwakwalwa wanda zai bawa Ruwanda damar karban uoro miliyon E1.5 daga kasar Faransa.
Kafin haka, a bangaren raya kasa samar da ayyukan yi kuma kasashen biyu sun rattabawa hannu kan bashin uoro miliyon 60.
342/